1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan cikin jaridun Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
May 19, 2023

Yunkurin kasashen Afirka na son sulhunta Rasha da Ukraine da rikicin Sudan, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/4Rb31
Rasha | Afirka | Taro | 2019 | Dangantaka
Akwai dadaddiyar dangantaka tsakanin Rasha da AfirkaHoto: picture alliance/dpa/Kremlin

Za mu fara ne da jaridar die tageszeitung da ta tsara sharhi mai taken "Afirka na son shiga tsakanin Moscow da Kyiv", inda ta ce Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya sanar da ziyarar aiki da wasu shugabannin kasashen Afirka shida za su gudanar, domin ganawa da Shugaba Vladimir Putin na Rashan da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da amincewarsu a wani yunkuri na diflomasiyya da nufin kawo karshen yaki tsakanin Rashan da Ukraine. Jaridar ta ce wanda ba zai iya kasa a gwiwa wajen zuwa kasar Rasha ba shi ne  shugaban Yuganda Yoweri Museveni saboda a kwanakin baya dansa Muhoozi Kainerugaba da ke da karfin fada a ji a rundunar sojojin kasar, ya yi tayin aika dakaru zuwa Moscow domin kare babban birnin kasar Rasha daga hari. Ita ma Afirka ta Kudu ta tsaya tsayin daka kan hadin gwiwarta na sojoji da Rasha, duk da suka da ta sha. Sannan ana tafka muhawara tun a watan Maris kan ko Afirka ta Kudu za ta aiwatar da sammacin kotun hukunta manyan laifukan yaki ta kasa da kasa, na kama Putin idan ya zo zaman taron BRICS a watan Agusta kan ta'asar da ya aikata a Ukraine.

Sudan | Rikici | Khartum | Darfur
Har yanzu ana ci gaba da musayar wuta a SudanHoto: via REUTERS

A game da rikicin kasar Sudan kuwa, jaridun Jamus biyu ne suka yi tsokaci a kai a wannan mako. Na farko dai ita ce Süddeutsche Zeitung da ta yi sharhi mai taken "Tarkon mutuwa a cikin fadin yankin Darfur", inda ta ce a yayin da bangarorin da ke rikici da juna a birnin Khartum ke shawarwarin tsagaita bude wuta, tashe-tashen hankula na kara kamari a Darfur da ke yammacin Sudan. Ta kara da cewa duk da yarjejeniyar kare fararen hula daga yakin da manyan janar-janar na Sudan din da ke yakar juna suka cimma, amma tashin hankalin ya ci gaba da ruruwa musamman a Darfur inda ake samun wuce gona da iri yayin da hankali ya karkata kan Khartoum. Ta ce hadarin kisan kiyashi a kan fararen hula na kabila marasa rinjaye, na dada karuwa. Ita kuwa Die Zeit a sharhinta mai taken "Tserewa ko zama? ta ce rikicin Sudan ne zai zama rikicin 'yan gudun hijira na gaba saboda a daidai lokacin da hukumomin agaji ke kokarin taimaka wa da abinci da magunguna, masu rikici da juna na gwabza fada tare da wawushe kayayyakin taimakon da aka samar. Jaridar ta kara da cewa duk jerin sanarwar tsagaita bude wuta da kare fararen hula sun zama tamkar izgili, saboda fiye da mutane dubu 700 ne suka guje wa yakin yayin da fiye da dubu 200 suka shiga kasashen da ke makwabtaka da Sudan.

Mali | undunar Wanzar da Zaman Lafiya | Majalisar Dinkin Duniya | Makoma
Makomar Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a MaliHoto: SIA KAMBOU/AFP

A daya hannun kuma, die tageszeitung ta maida hankali kan takun saka tsakanin Majalisar Ddinkin Duniya da kasar Mali. Ta ce yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta zargi sojojin Mali da sojojin hayar Rasha na Wagner da kashe fararen hula fiye da 500 a kauyen Mura da ke lardin Mopti gwamnatin Bamako ta fusata a kan wannan batu, inda ta bayyana matakin da "leken asiri da kuma makirci". Jarida ta nuna kokwanto kan makomar rundunar kiyaye zaman lafiya a Mali saboda tsawaita wa'adinta da zai kare a ranar 30 ga Yuni, zai gudana ne a yanayi mai sarkakiya. Sannan zai iya tasiri a kan matakin da Jamus za ta dauka, game da dakarunta da ke Mali. Fadar mulki ta Berlin na son majalisar dokokinta ta Bundestag, ta sake tsawaita aikin sojojin Bundeswehr har zuwa watan Yunin shekar ta 2024.

Jamus | Najeriya | Benin | Kayan Tarihi | Makoma
Makomar kayan tarihin masarautar birnin Benin na Najeriya da Jamus ta mayarHoto: Wolfgang Kumm/dpa/picture alliance

Idan muka koma fannin raya al'adu kuwa, jaridar WELTplus ta dasa ayar tambaya, inda ta ce: Shin kayayykin tarihin na masara'autar Benin da suka rikide zuwa mallakin wasu mutane, za su bace ne ko kuma suna fuskantar barazanar lalacewa? A bayanin da ta yi, ta ce cikin hanzari Shugaba Buhari na Tarayyar Najeriya ya dauki matakin mika kayayyakin na tagulla ga Oba Ewuare II na Benin ba tare da fayyace muhimman tambayoyi kan makomarsu ba.