Jamus: Zanga-zangar kawar da ra′ayin kyamar baki | Labarai | DW | 13.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Zanga-zangar kawar da ra'ayin kyamar baki

Dubban masu zanga-zanga ne suka yi wa tsakiyar birnin Berlin tsinke, don nuna goyon bayansu ga kokarin kawar da akidar nan ta tsatsauran ra'ayin kyamar baki.

Hakan na zuwa ne bayan wani mai akidar ta kyamar baki ya afka wa wasu Yahudawa a wajen ibada ranar Larabar da ta gabata a birnin Halle da ke gabashin Jamus, inda ya hallaka mutum biyu.Wadanda suka shirya gangamin da ke da'awar zama ba tare da bambamci ba, sun ce mutum dubu 13 suka halarci gangamin.