1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A wannan Lahadin ake gudanar da zabe na jihar Hessen

Ramatu Garba Baba
October 28, 2018

Al'umar jihar Hessen na cigaba da kada kuri'unsu a wannan Lahadin inda sakamakon zaben zai iya yin tasiri ga dorewar jam'iyyar CDU mai mulki ta Angela Merkel.

https://p.dw.com/p/37HOG
Deutschland Hessen Landtagswahlen
Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Jam'iyyar ta CDU ta kwashi tsawon shekaru goma sha tara ta na samun rinjaye a Hessen, rashin nasarar ka iya yin nakasu ga gwamnatin hadakar da aka samar a watan Maris. Makonnin biyu da suka gabata jam'iyyar ta CSU ta fuskanci mummunan koma baya a zaben jihar Bavaria inda 'ya'yan jam'iyyar suka yi sauyin sheka zuwa jam'iyyar The Green ta masu rajin kare muhalli, daga karshe ta yi nasara bayan da ta zarta matsayin da take da shi a can baya a Bavarian, ana kyauta zaton ta kuma bayar da mamaki a Hessen ganin yadda ta kama hanyar zama babbar jam'iyya ta biyu koda a matakin tarayya. An dai zura ido kan zaben na yankin da ke da yawan al'umma akalla miliyan shida.