1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamus za ta maida wa Najeriya kayan tarihinta

Ramatu Garba Baba
April 30, 2021

Jamus ta shirya mayar da wasu kayan tarihi mallakar masarautar Benin da ke Kudancin Najeriya da aka karbe a lokacin mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/3sn2T
Benin | Geraubte Kulturgüter aus der Kolonialzeit
Hoto: Wolfgang Kluge/picture alliance

Jamus ta kasance daya daga cikin kasashen da ta yi cinikin wadannan kayan ma su daraja da kuma dimbin tarihi, daga hannun wasu kasashen Turai da suka karbe kayan daga Afirka, kuma tuni ta dauki matakin shirya yadda za a mayar da kayan ainihin asalinsu. Ministan harkokin wajen Jamus, Heiko Maas, ya ce, cimma matsaya na mayar ma Najeriya kayan, wani sabon babi ne na shawo kan kuskuren tarihi da aka tafka a baya.

Tagullan na Benin, suna tattare da tarihi irin na mulkin danniya da aka yi ma jama'a a wancan lokacin. An shirya mayar da wadannan kayayyakin Najeriya a shekarar 2022 mai zuwa kamar yadda gwamnatin Jamus din ta sanar. Kayan suna nuna yanayi na rayuwar yau da kullum da kuma yanayin yaki.

Jamus ta amince a yi abin da ta ce, shi ne adalci, an wawushe wadannan kayan daga akasarin kasashen da aka yi ma mulkin mallaka Afrika a karni na sha tara, kayan al'adun gargajiyar da aka fi sani da Benin Bronzes, an sayar da su ga kasashen Turai da suka nuna sha'awarsu.

Dakin adana kayan tarihin Jamus na birnin Berlin yana dauke da wadannan kayan kimanin 530 baya ga gumaka na tagulla kimanin 440 na masarautar Benin da ke yankin kudancin Najeriya. An kiyasta cewa, an yi awon gaba da wadannan kayan a shekarar 1897.