Jamus: Za mu hada ′yan hijira da iyalansu | Labarai | DW | 11.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Za mu hada 'yan hijira da iyalansu

Kasar Jamus ta kare matsayinta na hada iyalan wadanda rikici ya tilasta su zaman hijira a kasarta daga kasashen da ke fama da yake-yake.

Gwammnatin kasar Jamus ta kare matsayinta na hada iyalan wadanda rikici ya tilasta su zaman hijira a kasarta. Akalla dai akwai kananan yara dubu uku da kuma manyan 1,500 da gwamnatin Jamus din ta amince masu su shigo kasar kafin daga bisani su wuce kasar Girka. Ma'aikatar cikin gida ta ce an ma sami jinkiri ne saboda wasu matsaloli ta fuskar tsare-tsare da aka fuskanta.

Ita ma dai gwamnatin kasar Girka ta ce tana fuskantar matsalar karancin ma'aikatan da za su dace da yawan masu neman mafakar. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a bana kadai, kimanin baki dubu 140 ne suka shigo nan nahiyar Turai ta teku, galibinsu kuwa ta kasar Italiya.