1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba da matakin kare muhalli a Jamus

Ramatu Garba Baba
November 26, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ce ta yaba da matakin da gwamnatin Jamus ke dauka don ganin ta kare muhalli daga illolin da Sauyin yanayi ke haifarwa.

https://p.dw.com/p/3TmVy
2019 Internet Governance Forum in Berlin
Hoto: Reuters/F. Bensch

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yaba da tsarin da gwamnatin Jamus ta bijiro don ganin an kare muhalli, babban jami'in ya fadi hakan ne a yayin wata ganawa da yayi da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a wannan Talata a fadar gwamnati da ke a birnin Berlin. 

Guterres ya ce, kasar ta zama abin koyi ga sauran kasashen duniya bisa gwagwarmayar da ta sa gaba na ganin an kare duniya daga illolin da Sauyin yanayi ke haifarwa inda ya nemi sauran kasashen duniya da subi sahun Jamus.

Tsarin da ke ci gaba da fuskantar suka, na son ganin an rage hayakin Carbon daga ababen hawa da makamashi a nan da shekara ta 2050 domin tsaftace muhalli daga gurbatacciyar iskar.