1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhunta rikicin Libya a Berlin

Abdullahi Tanko Bala
January 15, 2020

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas yace yana da kwarin gwiwar za a cimma yarjejeniyar sulhunta rikicin kasar Libya a babban taron duniya da za a gudanar a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/3WDlk
Berlin - Angela Merkel trifft Libyschen Premierminister Fayez al-Sarraj
Hoto: picture-alliance/AA/A. Hosbas

Heiko Maas yace a halin da ake ciki an kai wani matsayi da za a iya cimma yarjejeniyar wadda ta hada da dukkan masu ruwa da tsaki a cikin lamarin. A saboda haka yace zai kasance abu mai ma'ana a hadu baki daya a babban taron na kasa da kasa don samun masalaha ta siyasa amma ba da karfin soji ba.

Maas ya shaidawa 'yan jarida cewa matsayin gwamnatin Jamus shine cewa za a kawo karshen rikicin cikin sauki idan aka kawar da tasirin da ake samu daga waje sannan wadanda ke marawa bangarorin da ke gaba da juna suka daina samar musu da makamai.

Yarjejejniyar da za a cimma a taron na Berlin za ta share fagen kawo karshen yakin basasar tare yin hani ga wadanda ke da hannu a cikin yakin su tada dukkan wata fitina a nan gaba.