Jamus ta gargadi Turkiyya kan Tekun Bahar Rum | Labarai | DW | 19.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta gargadi Turkiyya kan Tekun Bahar Rum

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ce akwai yuwar kungiyar tarayyar Turai ta sake kakabawa gwamnatin Ankara takunkumi, idan ba ta jdena haddasa rikici a gabashin Tekun Bahar Rum ba.

Gwamnatin Jamus ta gargadin Turkiyya ta rage haddasa rikici a gabashin Tekun Bahar Rum in dai tana son tsira daga sabbin takunkumin kungiyar Tarayyar EU.

Da ya ke magana gabannin taron EU a watan Disamba, ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ce dabara ta rage wa Shugaba Raccep Tayyip Erdgang na daukar mataki domin kaucewa abin zai biyo baya, Maas ya ce ziyarar Erdogan a gabashin Cyprus alama ce ta nuna tirjiya.