An haifi Recep Tayyip Erdogan a shekarar 1954. Erdogan dan siyasa ne da ya yi fice a kasarsa ta haihuwa wato Turkiyya.
Erdogan ya rike mukamin firaminista daga shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2014 kuma a shekarar ta 2014 ne ya kasance mutum na farko da aka zaba a matsayin shugaban kasa. Erdogan na tare ne yanzu haka da jam'iyyar nan ta AKP.