1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta mayar wa Najeriya kayan tarihinta

Muhammad Bello MA
May 17, 2022

Kimanin kayayyakin tarihi dubu bakwai ne Jamus ta shirya maida wa masarautar Benin ta jihar Edo a kudancin Najeriya, bayan shekaru da dama da kwashe su.

https://p.dw.com/p/4BQet
Köln Ausstellung „I miss you“ im Rautenstrauch-Joest-Museum
Hoto: Fadi Elias

Tuni dai aka fara dawo da wasu daga cikin kayayyakin. Ko da yake an sha tirka-tirka tsakanin masarautar ta Benin da kuma bangaren gwamnatin jihar a Edo din kan wanda ke da alhakin karbar kayayyakin na tarihi. Daga baya dai an sulhunta tare da nunar da tsare-tsare da za su tabbatar da cewar wadannan kayayyakin tarihi an ci gaba da adana su ba tare da sun salwancewa ba.

A shekarar da ta gabata ta 2021 ne dai, wata tawaga daga Jamus karkashin jagorancin jakadan Najeriya a kasar ,ta yiwo takanas har fadar sarkin na Benin a jahar Edo, inda kuma aka fara mika wadannan kayayyakin tarihi daga cikin kayayyakin kimanin dubu bakwai ga masarautar.

Tun kafin kaiwa ga tantance inda ya kamata a mika wadannan kayayyakin tarihi da Jamus din ta kwashe shekaru aru-aru, sai da aka yi ta kai ruwa rana da bangaren gwamnatin jihar, inda gwamnatin ke ta kafewar cewar ita ya kamaci a bai wa kayayyakin, yayin da ita kuma masarauta ke cewar ita za a mika wa.

Benin | Museumsboom
Hoto: Katrin Gänsler/DW

Wannan yanayi dai ya sa an kwashe kwanaki ana ta tirka- tirka da ta sa tunani ga Jamus din da ma duk masu lura da al'amura, cewar tirka-tirkar somi ne na fara tafalilin salwantar da wadannan kayayyaki na tarihi.

To sai dai daga bisani an cimma maslaha, inda masarautar ta karbi wadannan kayayyaki, cikin tsari da mutunci da kuma alkawarin gina dakunan ajiye kayayyakin na tarihi don amfanin ma su ziyara daga ciki da wajen Najeriyar.

Tarihi dai ya tabbatar cewar kimanin kaso 90 cikin 100 na kayayyakin tarihin sassa daban-daban na Afrika na a nahiyar, bayan turawan yawon duniya sun kyalla ido sun gansu, tare kuma da jide su zuwa kasashensu.