1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na fargabar karuwar Corona

Abdul-raheem Hassan
September 21, 2020

Gwamnatin Jamus na fargabar karuwar annobar Corona a kasar bayan da ake samun yawaitar masu cutar a kasashe Faransa da Holland da Ostireliya.

https://p.dw.com/p/3ilwq
Gesundheitsminister Jens Spahn
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Becker

Ministan lafiya na kasar Jamus Jens Spahn ya ce yaduwar cutar a kasashen da Jamus ke makotaka da su ka iya rabar ta kowane lokaci.

Mutane sama da miliyan 30 sun kamu da cutar a duniya baki daya yayin da kusan miliyan guda suka rasu.

Kasar Amirka ce ke kan gaba da yawan masu dauke da ita, Indiya ke zama ta biyu, Brazil ce kasa ta uku a duniya da yawan masu dauke da cutar ta Covid-19 a duniya.