Zargin Rasha da kutse kan harkokin zabe a kasashen na yamma dai na ci gaba da karuwa, yayin da har kawo yanzu bincike bai tsaya ba kan zargin kasar ta Rasha da kutse kan harkoki na zaben Amirka.
Cibiyar leken asirin cikin gida a Jamus ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan alakar Rasha da wasu jam'iyyu na kasar ciki kuwa har da jam'iyyar AfD mai adawa da baki a kasar ta Jamus, kamar yadda gungun kamfanonin yada labarai na RND suka ba da rahoto a wannan Alhamis inda suka bayyana majiyar labarin nasu daga jami'an leken asirin.
Cibiyar leken asirin ta Jamus a matakin tarayya BfV ta cimma matsaya da rassanta a yankuna don sa idanu kan wannan zargi tun daga ranar Talata bayan da aka samu rahotanni Rasha na son kutse kan harkokin zabe a kasashen Turai a watan Mayu, da ma wasu zabukan na yankuna uku da za a yi a gabashin Jamus a wannan shekara a cewar kafofin yada labaran na RND.
Zargin Rasha da kutse kan harkokin zabe a kasashen na yamma dai na ci gaba da karuwa, yayin da har kawo yanzu bincike bai tsaya ba kan zargin kasar ta Rasha da kutse kan harkoki na zaben Amirka a shekarar 2016.