1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Matakai kan sinadaran kashe kwari

Zulaiha Abubakar
November 6, 2018

Ministar muhallin Jamus Svenja Schulze ta sanar da shirin gwamnatin kasar na fito da sabbin matakan amfani da sinadaran kashe kwari da ciyayi a kasar.

https://p.dw.com/p/37m2d
Bayer AG Logo
Hoto: picture-alliance/Geisler/C. Hardt

Kasashen Turai da Amirka sun jima suna tabka muhawara bisa zargin Sinadarin Glyposate na kamfanin Bayer AG da haddasa cutar sankara. A watan Fabrairun wannan shekara ne dai Jam'iyyar CDU wacce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke jagoranta tare da SPD Jam'iyyar hadaka suka amince da hanin amfani da sinadarin na Glyphosate ko da ya ke  ba a sanar da da lokaci ba. A halin yanzu dai ministar muhallin ta tabbatar da cewar hanin amfani da sinadarin a kusa da ruwa da sauran gurare ya fara aiki kuma zai cigaba da aiki har zuwa shekara ta 2023 lokacin da dokar haramcin amfani dashi za ta fara aiki.