1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Majalisar dokoki ta yi zaman karshe kafin zabe

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
September 5, 2017

Bisa ga al'ada zaman karshe na majalisar ta Bundestag na zama na waiwaye dangane da ci gaban da aka samu a wa'adin da ke shirin shudewa.

https://p.dw.com/p/2jNtp
Berlin Bundestagssitzung Rede Kanzlerin Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Stache

A wannan Talatar ce Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta yi zama da ke zama na karshe a wannan wa'adi na mulki. Wannan ya zo ne kwanaki kalilan kafin gudanar da zaben 'yan majalisa da zai ba da damar sabunta kujerun 'yan majalisar dokoki da kuma shugaban gwamnati. Saboda haka ne 'yan takara dabam-dabam sun yi amfani da wannan dama wajen sukar manufofin abokansu na siyasa.

Kasancewa Angela Merkel ta jam'iyyar CDU ce ta jagoranci gwamnatin Jamus na tsawon shekaru hudu, wakilan sauran jam'iyun sun yi ca a kanta dangane da batutuwa da dama. Daidai da jam'iyyar SPD da ke kawance da ta gwamnatin Merkel a yanzu ba a barta a baya ba kan salon kamun ludayin Merkel din.

Deutschland Bundestag Abstimmung über Ehe für Alle
Thomas Oppermann shugaban bangaren wakilan SPD a majalisar Bundestag Hoto: REUTERS/F. Bensch

Shugaban rukunin 'yan majalisar SPD da ke kawance da ta gwamnati Thomas Oppermann ya zargi shugaban gwamnati Angela Merkel da yin biris da wasu sauye-sauye da za su kawo wa jama'a ci gaba, inda ya ce sai da suka yi tsayuwar daka ne hakarsu ta samu ta cimma ruwa.

"Wannan gwamnatin ta ci gaba sosai a cikin shekaru hudu da suka gabata, kuma mun kafa wasu dokokin da suka sauya rayuwar mutane da yawa a wannan kasa, saboda haka dole in ce ina alfahari da abin da muka cimma tare.  Amma gaskiyar ita ce, dukan wadannan ci gaban mu 'yan jam'iyyar SPD ne muka samar da su, bayan da muka yaki abokan huldarmu na CDU da CSU."

Ita ma Sahra Wagenknecht, jagorar jam'iyar die Linke a Bundestag ta bi sahu wajen caccakar manufofin shugabar gwamnatin Jamus, inda ta zargi Merkel da hana ruwa guda dangane da wasu manufofin da 'yan adawa suka sa a gaba, lamarin da ta ce ya saba wa tsarin dimokuradiyya.

"Dole ne in gaya miki cewa, kin kasance a yanzu kuma a gaba wata barazana ga ci gaban al'umma, ko da a lokacin da Jamus ke samun habakar tattalin arziki, ko kuma a lokacin da duniya ke fuskantar kalubale iri dabam-dabam. A cikin wannan yanayi ne kike kokarin hana muhawara kamar yadda dimokuradiyya ta tanada, domin samun mafita game da wadannan matsaloli tun da sauri. Ina jin cewa wannan ba karamin abin takaici ba ne. "

Berlin Bundestagssitzung Rede Kanzlerin Merkel
Merkel: "muna daukan matakan bai daya na dakile kwararowar baki"Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Sai dai shugabar gwamnatin Jamus kuma 'yar takarar jam'iyyar CDU/CSU ta wanke kanta daga zarge-zargen da aka yi mata kama daga kan rikici da Turkiyya har zuwa badakalar gurbataciyyar iska a motocin da Jamus ke kerawa da batun bakin haure. Tun bayan da Merkel ta bude kofofin Jamus ga dubban 'yan gudun hijirar Siriya da kasashen Afirka da ke fama da yaki take shan suka kan wannan batu. Sai dai ta ce ita da takwarorinta na Turai suna daukan matakai na bai daya na ja wa 'yan Afirka da ke shigowa ta barauniyar hanya birki.


"Mun dauki matakai da dama a kan wannan batu. Na nuna sha'awa ga hadin gwiwa da Afirka. Mun tattauna da Italiya, da Spain da Faransa a kwanan nan game da yarjejeniyar da muka cimma da gwamnatocin Libiya, Nijar, Chadi da sauran kasashen Afirka. Game da gwamnatocin kama karya kuwa, ban ki cewa salonsu ya saba wa tsarin dimokuradiyya ba, amma kuma duk da haka dole mu yi magana da wadannan kasashe. Za mu gudanar da taron EU da Afrika a karshen shekara kuma a wannan taron ne za a yi aiki, don inganta cinikayya tare da Afirka, don ci gaban tattalin arziki a Afirka. "

Batu guda da daukacin 'yan majalisar suka nuna bakin cikinsu a kai shi ne samu goyon baya da jam'iyyar AfD da ke kyamar baki ke yi a sassa dabam-dabam na Jamus.