Jamus: IS ta yin yinkurin kai hari a birnin Munich | Labarai | DW | 01.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: IS ta yin yinkurin kai hari a birnin Munich

Hukumomin 'yan sandar birnin Munich na Jamus sun bayana cewa wasu bayanan sirri sun nuna cewa Kungiyar IS ta yi yinkurin kawo hari a birnin Munich na Kudancin kasar a daren jiya jajibirin shiga sabuwar shekara ta 2016

Hukumomin 'yan sandar birnin Munich a nan Jamus sun bayyana cewar wasu bayanai da suka samu daga hukumomin leken asiri na wasu kasashe makobtan kasar ta Jamus sun nunar da cewa Kungiyar IS ta yi yinkurin kaddamar da harin kunar bakin wake a birnin Munich na Kudancin kasar a daren jajibirin shiga sabuwar shekarar miladiya 2016.Babban jami'in 'yan sanda na birnin na Munich Hubertus Andrä ya bayyana hakan lokacin wani taron manema labarai da ya gudanar a a cikin daren Alhamis washe garin wannan Jumma'a tare da ministan cikin gida na jihar Bavaria Joachim Herrmann

Hukumar 'yan sandar birnin na Munich ta ce ta gano rukunin wasu mutane biyar da take zargi da yiwuwar su kai harin. Sai dai ta ce kawo yanzu ba ta dakatar da ko da mutun daya ne daga cikinsu ba. An dai ta dauki matakin rufe babbar tashar jirgin kasa ta birnin dama kuma wata tashar ta biyu ta Pasing da ke a Yammacin birnin tare da gargadin jama'a da su kaurace wa yin taruka ko kuma shiga ababen safara na gama gari .