Jamus gabanin hadewa da bayan hadewa
Jamus ta shafe shekaru tana rabe, abubuwa da dama sun sauya tun bayan sake hadewa. Ga wasu daga cikin sauye-sauyen da aka samu daga jinjina daga Berlin da Potsdam zuwa Stralsund gami da wasu wurare.
Kofar Brandenburg
An gina Kofar Brandenburg a 1791, wuri mafi shahara a birnin Berlin. Ya kasance iyaka tsakanin Gabashi da Yammacin Jamus yayin da birnin yake rabe. Bangaren gabashin ya kasance inda yake rufe ga 'yan Yamma. Amma lamarin ya sauya bayan faduwar katangar Berlin a shekarar 1989 inda babu sauran rabuwa. Yanzu miliyoyin mutane daga Jamus da sauran sassan duniya suna kai ziyara wajen mai tarihi.
Katangar Berlin
A tsawon shekaru 28 Katangar Berlin ta raba birnin tsakanin Gabas da Yamma. Mutane da dama sun hallaka yayin yunkurin tsallake katangar mai tsawon kilomita 155, da ke karkashin matakan tsaro, akwai mutane da dama da suka jikkata. An yi zane a bangaren gabashin katangar. Masu zane daga Jamus da sauran sassan duniya suka yi a shekarar da kasar ta sake hadewa.
Gidan fursuna na Hohenschönhausen
Har zuwa 1989, gidan fursuna na Hohenschönhausen ya kasance babban gidan yari da 'yan sandan ciki na Jamus ta Gabas suke amfani da shi. Ana gana azaba ga fursunonin siyasa. Inda gidan yarin yake ya kasance babban sirri kuma ba ya cikin taswirar birnin. An rufe shi bayan sake hadewa sannan aka bude daga bisani a matsayin wajen tuna baya.
Fadar Berlin
A Jamus ta Gabas, "The Palace of the Republic" ya zama wajen nuna karfi. Bayan budewa a 1976, ya kasance wajen yin taruka na siyasa. A shekara ta 2006 an rusa inda yanzu haka wajen yake karkashin sabon ginin da ake yi.
Mutum-mutumin Lenin a Berlin
Daga 1970 zuwa 1991, mutum-mutumi mai tsawon mita 19 ya kasance bangaren wata unguwa a gabashin Berlin da ake kira "Friedrichshain". Wannan ya zama dandali da aka sadaukar ga tsohon jagoran Tarayyar Sobiet Vladimir Lenin. Amma wannan karfe ya fadi lokacin da gwamnatin gabashin ta kawo karshe. Yanzu dandalin da ake kira na Lenin ya zama dandalin Majalisar Dinkin Duniya.
Wajen ajiye kaya na KaDeWe
Cikekken sunan "The Kaufhaus des Westens" a takaice "KaDeWe" wajen kaya mafi inganci a Jamus. Shi ne na biyu wajen girma a Turai bayan "Harrods" na birnin London. An bude wajen kayan kawan a shekarar 1907, kuma ya tsallake lalacewa lokacin yakin duniya na biyu. Ya kasance a bangaren Berlin ta Yamma lokacin da birnin ya dare gida biyu. Yau yana cikin wuraren yawon bude ido ga 'yan kasa da baki.
Wajen wasa
Babu abin da yara ke bukata kamar wajen wasa. Wannan karfen wasa na gefen (hannun hagu) ake gani a bangaren gabashi. Yanzu an sauya zuwa na igiya da ake wasa. Ana iya samun irin wannan hotuna a shafukan sada zumunta na birnin Berlin na Facebook: #GermanyThenNow and #BerlinThenNow.
Fadar Birnin Potsdam
Fadar mai tsari na musamman ta kasance wurin da mashahuren mutane suka yi rayuwa, da suka hada da Frederick William na I da Frederick the Great. Amma lokacin yakin duniya na biyu an rusa fadar sakamakon ruwan wuta. Gwamnatin Jamus ta Gabas ta rusa a 1959 zuwa 1960. Yau an sake ginawa a matsayin wajen tarihi.
Majami'ar Dresden
Ranar 15 ga watan Febrairun 1945 — kwana biyu bayan ruwan wuta na farko kan majami'ar Dresden ginin ya rushe. Shekaru 40 daga bisani majami'ar ta zama abin tuni kan illar yaki. Bayan faduwar Katangar Berlin an sake gina majami'ar - godiya daga masu ba da agaji a Jamus da sauran kasashen duniya.
Tsohon garin Stralsund
Garin Stralsund da ke Mecklenburg-Western Pomerania ya yi suna kan irin tsarin gine-gine da yake da su wadanda suka fuskanci barazana karkashin gwamnatin Jamus ta Gabas. Bayan sake hadewa an yi gyare-gyare. A shekara ta 2002 tsaffin gine-gine sun zama wajen tarihi na hukumar raya ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO.
Gadar Kogin Werra daga Vacha
Wannan gada ta Vacha da ke Thuringia da kauyen Philippsthal da ke Hesse kan Kogin Werra. Akwai katangar karfe da wayoyi a kogin, iyakar Jamus a cikin gida har zuwa 1989. Yau kowa na wucewa babu wata matsala inda ta zama "Kadar Hadin Kai".