1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FDP ta amince da shiga gwamnati

December 5, 2021

Jam'iyyar FDP ta amince da yarjejeniyar kulla kawance da jam'iyyun SPD da kuma The Greens kwanaki kalilan gabanin Olaf Scholz na SPD ya zama shugaban gwamnatin Jamus.

https://p.dw.com/p/43rvt
FDP Parteitag (Aufmacher)
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A babban taron jam'iyar ta FDP, mutane 535 ne suka kada kuri'ar amincewa yayin da wasu 37 suka kada ta kin amincewa, wanda hakan ta kai ta ga cimma adadin nasarar kaso kusan 100. 

Yarjejeniyar kulla kawancen mai dauke da shafukan 177 ta zayyana manufofin gwamnatin kawance uku na farko a Jamus, wanda ya hada da jam'iyyun na SPD da FDP da kuma Greens. 

Shekaru 4 da suka gabata dai jam'iyyar FDP ta ki amincewa da yin aiki tare da gwamnatin bayan ta fice daga tattaunawar kulla kawance da shugabar gwamnatin Jamus mai barin gado Angela Merkel.