1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cafke wani dan Rasha a Jamus

Zulaiha Abubakar
August 22, 2018

Jami'an tsaro a kasar Jamus sun cafke wani dan kasar Rasha wanda ake zargi da shirya harin bam a kasar bayan ya rikide zuwa mai tsattsauran ra'ayin addinin Islama .

https://p.dw.com/p/33ZvO
Symbolbild Polizei-Einsatz
Hoto: Imago/Revierfoto

Wani bincike da jami'an tsaro suka gudanar tun a shekara ta 2016 a gidan  wanda ake zargin mai suna Magomed-Ali C ya tabbatar da samun sinadaran hada bama-bamai makare a wani daki a gidansa. Sinadaran da aka gano a gidan Magomed-Ali C mai shekaru 31 a duniya mazaunin birnin Berlin, sun ksance irin wadanda 'yan ta'adda suke yin amfani dasu wajen kai hari a kasashen yammacin Turai.

Magomed Ali C zai gurfana gaban kuliya a ranar Alhamis mai zuwa don girbar abin da ya shuka, duk kuwa da cewar ya zuwa wannan lokaci masu gabatar da karar basu bayyana dalilinsu na jinkirta kamen wanda ake zargin ba tun a baya.