1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ba za ta iya cimma kudirinta na muhalli nan da 2030 ba

Abdullahi Tanko Bala
June 3, 2024

Kwamitin ba da shawara ga Jamus kan muhalli ya ce kasar na fuskantar hadarin kasa cimma kudirinta na rage gurbatar hayakin masana'antu nan da shekarar 2030

https://p.dw.com/p/4gbKr
Tashar makamashin Kwal a Gelsenkirchen a Jamus
Tashar makamashin Kwal a Gelsenkirchen a JamusHoto: picture-alliance/AP/M. Meissner

Kwamitin bada shawara kan sauyin yanayi a Jamus ya yi kiran samar da sabbin manufofi na rage hayakin masana'antu yana mai kashedin cewa ga dukkan alamu kasar ba za ta iya cimma kudirin da sanya a gaba na rage hayakin masana'antun nan da shekarar 2030 ba.

A wani rahoto da aka wallafa kwamitin kwararrun kan sauyin yanayi ya ce da kyar Jamus za ta iya cimma kudirinta na rage kashi 65 cikin dari na hayakin masana'antu zuwa karshen lokacin idan aka kwatanta da matakin shekarun 1990.

Binciken ya saba da bayanan ministan kare muhalli kuma mataimakin shugaban gwamnati Robert Habeck wanda a watan Maris din da ya gabata ya ce hasashen ma'aikatar muhalli ta tarayya ya nuna ana samun raguwar gurbatar hayakin masana'antu  kuma Jamus za ta cimma kudirinta.