1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamiin majalisar dinkin duniya ya tserewa rikici a sansanin Darfur

May 8, 2006
https://p.dw.com/p/BuzD

Shugaban hukumar jin kai na majalisar dinkin duniya dake ziyara a Darfur,yayi gargadin cewa,ba zaa samu zaman lafiya cikin sauki a yankin darfur ba,duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya hannu akai a makon daya gabata tsakanin gwamnatin Sudan da babbar kungiyar yan tawaye ta yankin.

Jan egeland yace,dole ne kasashen duniya da kuma bangarori da abin ya shafa su kara bada himma wajen ganin an kaddamar da wannan yarjejeniya.

Majalisar dinkin duniya ta sanarda cewa,mazauna yankin da yan tawaye suke rike da shi kusan 200,000 suka tsere cikin watanni uku na bayan nan,saboda sojin haya larabawa da suka tsananta kai hare hare a sansanonin da suke zaune.

A yau din nan ne kuma jamiin na majalisar dinkin duniya tare da wadanda suke mara masa baya,dole suka tsere daga wani sansanin yan gudun hijira a darfur din,bayan barkewar zanga zanga,inda suka farwa wani maaikacin agaji.

Dubban yan gudun hijira dake sansanin kalma,suna zanga zanga ne na neman a aika da dajkarun wanzar da zaman lafiya domin su kare su,daga nan ne kuma wata yar gudun hijirar ta zargi wani maaikacin agaji cewa shi dan janjaweed ne,sai rikici ya barke,inda dole jamiin na majalisar dinkin duniya da mukarrabansa suka tsere daga sansanin.