1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami kan Iran

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 8, 2026

Sojojin Isra'ila sun kakkabo makamai masu linzami da Iran ta harba wa kasar, tare da dakile harin Houthi daga Yemen.

https://p.dw.com/p/5EzE5
Yadda jami'an tsaro Isra'ila suka kewaye wani makami da Iran ta kai wa kasar hari da shi ranar Litinin 08.06.2026
Yadda jami'an tsaro Isra'ila suka kewaye wani makami da Iran ta kai wa kasar hari da shi ranar Litinin 08.06.2026Hoto: Rami Shlush/AP Photo/dpa/picture alliance

Isra'ila ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan kasar Iran a wannan Litinin, bayan bijirewa gargadin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi ma ta, na kaucewa mayar da martanin harin da Iran ta kai mata, bayan far wa Lebanon.

Gidan talabijin na kasar Iran ya rawaito cewa an jiyo karar tashin bama-bamai a birane uku na yammaci da tsakiyar kasar, ciki har da Tehran, babban birnin kasar, ba tare da karin bayanin irin barnar da harin ya yi ba.

Karin bayani:Hizbullah ta yi watsi da yarjejeniyar Isra'ila

Wannan hari na Isra'ila, na zama martani kan wanda Iran ta kai ma ta na makamai masu linzami 11 ranar Lahadi, wanda dakarunta suka kakkabo, ba tare da illata kowa a kasar ba.

Wani rahoto da kafar yada labaran Iran ta Fars ta wallafa, ya ce harin Isra'ila barnata cibiyar makamashi ta Karu, da ke kudu maso yammacin birnin Bandar-e-Mashahr, mai iyaka da kasar Iraqi, kamar yadda mataimakin gwamnan lardin Khuzestan ya tabbatar.

Karin bayani:Amurka da Iran sun sake yin musayar wuta a tsakaninsu 

To sai dai tun gabanin faruwar hakan, aka jiyo shugaba Donald Trump na Amurka na jan kunnen firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da a kul ya kuskura ya far wa Iran, domin gudun janyo tarnaki ga shirinsa na kokarin lalubo bakin zaren dakatar da yakin baki-daya, wanda ya haura kwanaki 100 ana gwabza shi.

Karin bayani: Iran ta gindaya sharadin amincewa da yarjejeniya da Amurka

A wani labarin kuma Isra'ila ta ce garkuwar sararin samaniyarta, ta kakkabo makamai masu linzami da Iran ta harba mata a wannan Litinin, kamar yadda rundunar tsaronta ta IDF ta sanar a dandalin Telegram.

Tuni al'ummar kasar suka fara gudun shiga maboya ta karkashin kasa don neman tsira, bayan gargadin da suka samu ta wayoyinsu na hannu.

Karin bayani:Iran ta amince ba za ta mallaki Makamin Nukiliya ba - Trump 

Haka zalika rundunar sojin Isra'ila ta ce 'yan tawayen Houthi na Yemen, masu samun goyon bayan Iran, sun kai ma ta farmaki da makamai masu linzami.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, ya ce birnin Jerusalem ya wayi gari da jin karar fashewar abubuwa sosai.