1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hizbullah ta yi watsi da yarjejeniyar Isra'ila

Abdullahi Tanko Bala
June 4, 2026

Kungiyar Hizbullah ta ce ba za ta amince da duk wata yarjejeniya da ta bai wa Isra'ila damar ci gaba da zama a kudancin Lebanon ba, yayin da Isra'ila kuma ta ce ba za ta janye ba

https://p.dw.com/p/5EsDi
Yankin Nabatäa a lokacin wani harin Isra'ila
Yankin Nabatäa a lokacin wani harin Isra'ila Hoto: Abbas Fakih/AFP

Kungiyar Hizbullah a yau Alhamis ta yi watsi da yarjejeniyar baya bayan nan da aka cimma tsakanin Isra'ila da gwamnatin Lebanon inda ta bukaci Isra'ila ta janye baki daya daga Lebanon yayin da cigaba da fadan ke kawo tsaiko  ga yunkurin kawo karshen yakin Iran.

Sanarwar ta Hizbullah na zuwa ne yayin da wani harin Isra'ila ya kashe mutane hudu a cewar hukumomin yankin. Sannan kuma wani jam'in kiyaye zaman lafiya na Majlisar Dinkin Duniya shi ma ya rasa ransa a musayar wuta da ta ritsa da shi.

Shugaban Hizbullah Naim Kassem a cikin wata sanarwa da aka gabatar ta akwatin talabijin ya baiyana tattaunawar da ake a matsayin abin takaici da tozartarwa.