Isra’ila ta ce dakarunta sun sake kutsawa cikin kudancin Lebanon yau don yaƙan ’yan Ƙungiyar Hizbullahi. | Labarai | DW | 31.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra’ila ta ce dakarunta sun sake kutsawa cikin kudancin Lebanon yau don yaƙan ’yan Ƙungiyar Hizbullahi.

Hukumar rundunar sojin Isra’ila, ta ce dakatunta sun sake kutsawa yau cikin kudancin Lebanon, musamman a yankin Aita Al-Shaab, inda rahotanni suka ce sun yi wata ƙazamar fafatawa da mayaƙan ƙungiyar Hizbullahi. Duk da sanarwar dakatad da kai hare-haren jiragen sama a Lebanon ɗin, har tsawon sa’o’i 48 da Isra’ilan ta bayar, rahotanni sun ce yau ma, jiragen samanta sun kai hare-hare a kudancin ƙasar. Da can dai Isra’ilan ta amince da dakatad da kai hare-haren jiragen saman ne, bayan wani harin da ta kai jiya a ƙauyen Qana, ya halaka fararen hula kusan 60, mafi yawansu kuma yara ƙanana da tsoffin mutane. Amma ta ce harin da ta jiragenta suka kai yau kusa da ƙauyen Taba, wato don mara wa dakarun igwanta baya ne, waɗanda ke ta ba ta kashi da ’yan ƙungiyar Hizbullahi a yankin.

Harin dai ya kuma lalata wata motar sojin Lebanon a wajen garin Tyre, abin da hukumar sojin Isra’ilan ta ce ta yi nadamarsa. Kawo yanzu dai, babu wani ƙarin haske a kan asarar da sojojin Lebanon ɗin suka yi sakamakon wannan harin.