Isra´ila ta ce ba zata tattauna da ´yan ta´adda ba | Labarai | DW | 08.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta ce ba zata tattauna da ´yan ta´adda ba

Isra´ila ta yi fatali da kiran da FM Falasdinawa Isma´il Haniyeh ya yi na a tsagaita bude wuta gaba daya a Zirin Gaza. Wani kakakin FM Isra´ila Ehud Olmert ya fada a Birnin Kudus cewa ba zasu tattauna da ´yan ta´adda ba. Kakakin ya ce da farko dole ne a sako sojan Isra´ila da sojojin sa kai na Falasdinawa suka yi garkuwa da shi makonni biyu da suka wuce. A yau dai rundunar sojin Isra´ila ta janye daga wasu sassa na arewacin Zirin Gaza bayan ta kwashe kwanaki da dama tana kai farmakin soji a yankin. Wani labarin da ya iso mana yanzu yanzu nan na cewa wata karamar yarinya Bafalasdiniya mai shekaru 6 da haihuwa ta rasu yayin da mutane 5 suka samu raunuka a wani harin da jiragin saman yakin Isra´ila ya kai akan wani gida dake arewacin birnin Gaza. Dazu kuwa Falasdinawa 4 aka kashe a wata musayar wuta da suka yi da dakarun Isra´ila a Zirin na Gaza.