INEC ta ce ta yi nasarar raba katunan zabe | Siyasa | DW | 23.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

INEC ta ce ta yi nasarar raba katunan zabe

Kwanaki biyar kafin zaben Najeriya, hukumar zaben kasar ta INEC ta ce ta yi nasarar raba katuna zuwa hannun a kalla kaso 82 cikin dari na masu zaben kasar su milliyan 68

Kakakin hukumar Nick Dazang dai ya ce ya zuwa yanzu hukumar INEC ta gamsu da biyan bukatar kowa kama daga masu siyasar dake ta caccaka ya zuwa yan zaben da ke ta korafi na samun katin mai tasiri. Tun bayan dage zaben dai a fadar Dazang din akalla kari na mutane miliyan 15 ne suka yi nasarar samun katin, abun kuma da ke zaman karin haske ga samuwar nasarar zaben kama daga masu adawar kasar da ita kanta jam'iyyar PDP dake a gaba cikin adawa da batun sabon tsarin.

“In ka duba akwai rata ta kusan mutane miliyan 15 na wadanda suka karbi waddanan katuna, a bangaren mu Alhamdu lillahi, domin tun can niyyar mu shine duk wanda muka yiwa rijista ya karbi wannan kati. Kawo yanzu mun cimma wannan buri domin ba yanda za'a karbi katunan nan dari bisa dari. Wasu sun riga mu gidan gaskiya, akwai wadanda ba zasu je su karbi katunan nan ba. Zan baka misali da nan Abuja inda jami'an mu ke zauwa rumfar bada katunan ba tare da masu karba sun zo ba".

Kawunan manyan jam'iyyun na rabe

Schild in einem Wahllokal in Nigeria

Hankula sun karkata ga zuwa wuraren zabe ranar asabar.

To sai dai kuma har ya zuwa yanzu kawuna tsakanin manyan jam'iyyun dake shirin fafatawar na rabe game da shirin rabon katin na kara rabewa gida gida tsakanin masu adawar dake fadin ta yaba da shirin yan zaben da kuma PDP dake fadin har yanzu da sauran gyara. Dr Haruna yarima dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar APC na kasa kuma a tunaninsa hukumar zaben ta kasa tayi rawar ganin cikin shirin dake iya kawo sauyi a kasar.

“Hukumar zabe tay i rabo mai kyau, saboda ba za'a taba samun dari bisa dari ba saboda wasu sun rasu wasu kuma ba zasu zo su karba ba. Kuma maganar injin karanta katun zaben mun gamsu da ita mun gamsu da aikinta. Mutanen PDP ne ke adawa saboda sun saba da magudi kuma magudin ba zai yiwu a bana ba".

Yunkurin neman gyara

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2

Jama'a na fatan yin zabe cikin kwanciyar hankali

Kokari na magudi ko kuma neman gyara a tunanin PDP jada hukumar zaben na zaman gyara kayanka a cewar Barrister Abdullahi Jalo dake zaman mataimakin kakakin PDP na kasa

“In mun ga kura kurai zamu fada, kuma kua kuran muke fada. Kuma da anyi wancan zabe to da ba za'a samu kaso 20 cikin dari. Bamu raba riga da INEC ba muna tare da ita bamu da wata hukumar data fita. Amma muna sonta ko bamu so in mun ga kura kurai zamu fada saboda gaba”

Tuni dai fagen siyasar kasar ke kara dumi kuma kowa ke dada damara da nufin tabbatar da zaben da babu irinsa. Miliyoyin 'yan zaben kasar ta Najeriya dai na tsakanin zaben cigaban da gwamnatin PDP ke tafiya kansa, da kuma sauyin da 'yan adawar kasar ta Najeriya ke alkawari yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin