Hungary ta daina tura iskar gas Ukraine | Labarai | DW | 26.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hungary ta daina tura iskar gas Ukraine

Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna rashin jin dadinta dangane da dakatar da tura iskar da kasar Hungary ta yi zuwa Ukraine daidai lokacin da sanyi hunturu ya fara bayyana a kasar.

EU din ta ce wannan matakin da Hungary din ta dauka abu ne da zai sake dagula halin matsi da ake ciki a Ukraine din musamman ma dai gabashin kasar wanda ke fuskantar rikici tsakanin dakarun gwamnati da 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha.

Mahukunatn Hungary din dai sun ce sun dau wannan mataki ne soboda bukatar gas din a kasarsu ta karu don haka dole ne su dakatar da turawa Ukraine.

To sai dai hakan na zuwa ne 'yan kwanaki kalilan da gudanar da wani taro tsakanin wakilan gwamnatin kasar da kamfanin nan na Gazprom na Rasha, har ma aka jiyo firaministan Hungary din Viktor Orban na cewa bai son wani abu komai kankantarsa da zai dagula dangatakarsa da Rasha.