Huldar Jamus da Birtaniya bayan Brexit | Labarai | DW | 05.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Huldar Jamus da Birtaniya bayan Brexit

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci hada kai dan kulla dangantaka tsakanin kasashen Jamus din da Birtaniya bayan kammala shirin fitar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai EU.

Deutschland Angela Merkel und Theresa May bei einer gemeinsamen Pressekonferenz (picture-alliance/Reuters/BREUEL-BILD/Jason Harrell)

Firaiministan Birtaniya, Theresa May tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Merkel ta ce wannan wata kyakkyawar manufa ce da Jamus ke shirin cimma da nufin mutunta alakar da ke tsakanin kasashen biyu fiye da wacce suke ciki a baya. Da take jawabi a birnin Hamburg da ke arewacin kasar, shugabar gwamnatin Jamus din ta bayyana cewa akwai tasiri mai karfi ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki da za su kulla da Birtaniya, ta kuma ce akwai bukatar hada karfi tsakaninsu domin inganta bangaren tsaro.

A yanzu dai kasar Birtaniya ta mika wa kungiyar Tarayyar Turai takardun bukatar fita daga EU, inda aka tsara kammala shirin a cikin shekaru biyu. A nasu bangaren kasashen na EU sun fara nazarin yadda huldarsu da Birtaniya za ta kasance bayan fitar tata musamman fannin da ya shafi kasuwanci da haraji da makamantansu.