1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ka'idodin dimukuradiyya da kishin kasa ga matasa

Salissou Boukari AMA(SB)
July 5, 2022

A Jamhuriyar Nijar, an kaddamar da horon sanin makamar siyasa da karfafa dimukuradiyya da kishin kasa ga matasan jam'iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hula.

https://p.dw.com/p/4Di7c
Ziyarar shugaba Mohamed Bazoum a Jamus yana ganawa da matasan kasar
Ziyarar shugaba Mohamed Bazoum a Jamus yana ganawa da matasan kasarHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Kungiyar fararen hula ta Alternative Espace Citoyen hadin gwiwa da ma'aikatar cikin gidan Nijar da tallafin cibiyar kula da harkokin dimukuradiyya ta kasar Nederland ne suka shirya shirin, don nazari kan cigaban da aka samu ta fannin dimukuradiyya sanin dokoki da kuma nuna kishin kasa, tun bayan zagayan farko na horon da ya tattara matasa 120 daga bangarori dabam-daban na jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da dabilan jami'a. Manyan 'yan siyasa da suka jima suna fafatawa a fagen siyasar Nijar irin su Zainabou Abani na daga cikin wadanda suka halarci horon, inda ta ce.

 Karin Bayani: Wacce alkibla siyasar kasar Nijar ta dosa?

"Sanin kowa ne batun bayar da horo ga matasa batu ne da koda yaushe ake ganin cewa kishin kasa ya kyautu a saka shi a zukatan yara kanana tun suna azuzuwan farko na makarantun boko amma kuma lamarin ba haka yake ba a kasar ta Nijar, inda sai daga bisani ne ake kokarin neman tankwara karfe wanda tun da zafin shi ba a samu aka lankwasa shi ba."

Jami'ar zabe | Niger | Zaben shugaban kasa | a runfar zabe
Jami'ar zabe | Niger | Zaben shugaban kasa | a runfar zabeHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Tuni wadanda suka samu wannan horo na farko suka kasance tare da sabbin wadanda aka zaba a wannan karon don raba sani da ilimin da suka koya ga 'yan uwansu matasa na cikin jam’iyyu ko kuma kungiyoyin fararen hula da ma daliban jami'a, ciki har da Mahamadou Seidou Gajere dalibi a jami’ar birnin Yamai wanda yace "Idan aka yi la’akari da yawan jam'iyyun siyasar da Nijar ta ke da kuma a ce matasa ba su da sani kan harkokin siyasa da dimukuradiyya abun kumya ne."

Karin Bayani: Jam'iyyar MPN ta jingine adawa a Nijar

Abun jira a gani shi ne irin darasin da su kansu jam’iyyun siyasa a Jamhuriyar Nijar za su dauka daga fusa’ar kungiyoyin fararen hula da suke ganin ya kyautu matasa su samu horo kan sanin kishin kasa da yadda ake tafiyar da harkokin siyasa ko nan gaba a samu babban sauyi a fagen siyasar kasar ta Nijar da a yanzu yan siyasar ke mayar da shiga siyasa a matsayin wurin yin arziki ba wai sadaukar da kai wajen taimaka wa kasa ba.