Nijar: Wacce alkibla siyasar kasar ta dosa? | BATUTUWA | DW | 03.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Nijar: Wacce alkibla siyasar kasar ta dosa?

A Jamhuriyar Nijar, jam'iyyun MNSD Nasara da MPR Jamhuriya sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar jam'iyya mai mulki Malam Bazoum Mohamed a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

Niger Wahlen Seini Oumarou

Seini Oumarou zai mara wa Bazoum Mohamed baya a zaben Nijar zagaye na biyu

Jam'iyyun sun bayyana matsayarsu ne cikin sanarwar bayan taro da kowannensu ya shirya, a birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar. A yayin taronta da ya hada mambobin kwamitin zartarwa, jam'iyyar ta MNSD Nasara ta kuma kada kuri'a daga wakilan jihohi na jam'iyyar, inda shugabannin jam'iyyar 246 daga cikin 247 suka amince da mara wa dan takarar jama'iyya mai mulki ta PNDS Tarayyar Bazoum Mohamed baya a zabe zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 21 ga wannan wata na Fabrairu. 

Karin Bayani: Kotu ta hana madugun adawa takara 

Dama dai jam'iyyar ta MNSD Nasara wacce tazo ta uku a zagayen farko na zaben shugaban kasar da kuma ta samu kujeru 13 a majalisa, na cikin kawancen mulki da jam'iyyar PNDS Tarayya a yanzu haka. Jam'iyyar ta ce ta yanke shawarar ci gaba da zama tare da abokiyar tata, ta la'akari da yadda tsarin dan takarar jam'iyyar mai mulki ke kama da nata.

Niger - Politiker Albade Abouba

Albade Abouba shugaban jam'iyyar adawa ta MPR Jamhuriya a Nijart

Ita ma daga nata bangare jam'iyyar Malam Albade Abuba wato MPR Jamhuriya da ta zo ta hudu a zagayen farko na zaben shugaban kasa da kuma ke da kujeru 13 a majalisa, ta bayyana nata goyon bayan ga dan takarar jam'iyyar mai mulki Malam Bazoum Mohamed a wata sanarwa da ta fitar a Yamai babban birnin Jamhuriyar ta Nijar, lamarin da ke nuni da cewa tun kafin a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki da kawancenta na da gagarumin rinjaye a majalisa da kujeru sama da 130 daga cikin kujeru 165, wanda hakan zai ba su damar kafa gwamnati da mallake majalisa ko da jam'iyyar ta Tarayya ta sha kaye a  zagaye na biyu na zaben da za a gudanar ranar 21 ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin