Kotu a Nijar ta hana madugun adawa takara | BATUTUWA | DW | 13.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kotu a Nijar ta hana madugun adawa takara

Kotun kolin Jamhuriyar Nijar ta yi tankade da rairaya na 'yan takara da suka cancanci tsayawa a zaben shugaban kasar, inda babban madugun adawar kasar Hama Amadou ke cikin wadanda kotun ta hana damar yin takarar.

Hama Amadou

Kotu a Jamhuriyar NIjar, ta hana Hama Amadou yin takarar shugaban kasa

Wannan hukunci na kotun tsarin mulkin kasar dai, na zuwa ne a daidai lokacin da wasu mutane hudu ciki har da madugun adawar na Jamhuriyar ta NIjar da kotun tsarin mulkin ta hana damar tsayawa takarar shugabancin kasar, wato Hama Amadou suka shigar da wata kara gaban kuliya, suna bukatarkotun tsarin mulkin da ta jinkirta bayar da sakamakon tantance 'yan takarar. Sun dai bukaci a jinkirta sanar da tantance 'yan takarar shugaban kasar ne, sakamakon kalubalantar sahihancin takardun kasancewar dan kasa na Mohamed Bazoum dan takarar na jam'iyyar PNDS Tarayya da ke mulki a kasar.

Sai dai za a iya cewa kallo ya oma sama, domin kuwa dan takarar na jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Bazoum ya haye siradi, yayin da abokin hamayyarsa na babbar jam'iyyar adawar kasar wato Lumana Afirka Hama Amadou ya kasance cikin 'yan takarar da aka yi watsi da bukatunsu na yin takararr shugaban kasa a Jamhuriyar ta NIjar. Kawo yanzu dai, Hama Amadou da jam'iyyarsa ta Lumana ba su ce komai dangane da wannan hukunci, kana rahotanni sun nunar da cewa Hama ba ya kasar ya na makwabciyarta Tarayyar Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin