Hama Amadou daya ne daga cikin fitattun 'yan siyasa na Jamhriyar Nijar. A wani lokaci a baya ya taba rike mukamin kakakin majalisar dokokin kasar.
A cikin shekarar 2016 Malam Hama Amadou ya yi takarar shugabancin kasar karkashin inuwar jam'iyyar Moden Lumana Afrika inda ya zo na biyu a zaben sai dai ya yi watsi da sakamakon zaben inda ya yi zargin an tafka magudi.