Zaben Nijar ya bar baya da kura | Siyasa | DW | 25.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben Nijar ya bar baya da kura

Tarzomar bayan zabe da ta barke a Jamhuriyar Nijar bayan nasarar Bazoum Mohamed na PNDS-taryya ta yi sanadiyyar mutuwar wani jami’i, lamarin da ya sa hukumomi daukan matakan a kan wadanda ake zargi da marar hannu a boren

Watsi da sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da Mahamane Ousmane dan takarar adawa ya yi, ya haddasa tashin hankali a Yamai babban birni da wasu garuruwa na Jamhuriyar Nijar. Magoya bayan 'yan adawa sun yi bore ko da shi ke hukumomi sun kwantar da kurar rikicin tare da kame wasu kusoshin 'yan adawa da ake zargi da hura wutar rikicin. A mafi yawan lokuta dai, wanda ya sha kaye ya saba kalubalantar sakamakon zaben shuganan kasa a Nijar.

DW.COM