Nijar: Taro kan yin zabe cikin lumana | Siyasa | DW | 19.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Taro kan yin zabe cikin lumana

An bude wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe a Nijar, wanda Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin EU da ECOWAS da kuma CEN-SAD suka shirya.

Niger Wahlzentrale Niamey

Cibiyar Hukumar Zabe ta Kasa a Jamhuriyar Nijar, CENI

Taron wanda aka shirya shi a kan fadakar da al'ummar Jamhuriyar ta  Nijar game da muhimmancin gudanar da zabe cikin lumana, na zuwa ne a daidai lokacin da babban zaben kasar ke kara karatowa. A jawabin da suka gabatar a wurin bikin bude wannan taro, daya ayan daya dukkanin wakillan kungiyoyin na kasa da kasa da suka shirya shi sun tunatar da al'ummar ta Nijar musamman 'yan siyasa, hadarin da ke tattare da rigingimun zabe ga makomar kasa da ma tafarkin dimukuradiyya.

Karin Bayani: Rikicin cikin gida a jam'iyyar Lumana Afrika a Nijar

A nasa jawabin manzon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Sahel, Mohamed Ibn Chambas jan hankali ya yi ga 'yan jarida yana mai cewa: "'Yan jarida suna da rawar da ya kamata su taka a cikin harkokin zabe. Sakonnin da za ku yada tabarya ce mai baki biyu, ko dai su tabbar da kwanciyar hankali ko kuma su haifar da rudani a cikin tsarin zaben. Lokacin da ya rage 'yan makonni a gudanar da zabe, ya kamata sakonninku su zama na zaman lafiya da hada kan 'yan kasa. A kan haka nake kira ga duk masu ruwa da tsaki a harkokin zaben da su guji tashin hankali da yada kalaman kyamar juna."

Mohamed Ibn Chambas

Mohamed Ibn Chambas wakilin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya

Taron ya samu halartar wasu daga cikin 'yan takara a zaben shugaban kasa na tafe, haka ma wakillan kungiyoyin addinai da na sarakunan gargajiya na daga cikin mahalarta wannan taro. To sai dai daga nashi bangare Malam Tahiru Gimba na jam'iyyar Model Ma'aiakata da ya kasance cikin wadanda kotu ta hana su yin takara a zaben shugaban kasa, cewa ya yi da wuya wannan taro ya iya shawo kan matsalolin da ke tattare da wadannan zabuka.

Karin Bayani: Masana dokoki a Nijar na fuskantar barazana

Yanzu dai 'yan kasa sun zura ido su ga yadda za ta kaya a wannan taro da kuma tasirin da zai yi wajen yayyafa ruwa ga wutar rikicin zaben da ke ci gaba da ruruwa a tsakanin 'yan siyasar kasar ta Nijar, a daidai lokacin da ya rage 'yan makonni a gudanar da babban zabe na gama-gari.

Sauti da bidiyo akan labarin