Nijar: Rikicin cikin gida na jam′iyyar Lumana Afrika bai kare ba | Siyasa | DW | 21.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Rikicin cikin gida na jam'iyyar Lumana Afrika bai kare ba

Bisa dukkan alamu tsugune tashi ba ta kare ba a game da rikicin cikin gida na babbar jam’iyyar adawa a Nijar, Lumana Afrika, inda kowane bangare ya gudanar da nashi babban taro.

Ba dai tare da wata jayayya ba ce taron congres na jam'iyyar ta Lumana Afrika bangaren da ke goyon bayan Malam Hama Amadou da ya gudana a karshen mako a birnin Dosso ya kaddamar da Hama Amadou a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben shugaban kasa da ke tafe. Wannan kuwa duk da barazanar da takarar tasa ke fuskanta a gaban kuliya.

To sai dai daga nashi bangaren jam'iyyar ta Lumana da ke goyon bayan shugaban jam'iyyar na riko Malam Umaru Nom ya gudanar da garambawul ga kwamitin gudanarwa na jam'iyyar tare da kafa sabon kwamiti kana ya nada Malam Umaru Noman a matsayin cikakken shugaban jam'iyyar na kasa baki daya a maimakon mukamin shugaban riko da yake rike da shi a baya, kana dan takarar jam'iyyar a zaben na tafe.

Sai dai kuma a taron congres din nasa bangaren jam'iyyar ta Lumana da ke goyon bayan Malam Hama Amadou ya dauki matakin dakatar da wasu ‘ya'yan jam'iyyar na bangaren Umaru Noma a cewar Malam Bana Ibrahim daya daga cikin masu goyon bayan Hamma Amadou.

Hama Amadou da ke samun goyon bayan wani bangare na jam'iyyar Lumana Afrika

Hama Amadou da ke samun goyon bayan wani bangare na jam'iyyar Lumana Afrika

To amma da yake mayar da martani kan batun dakatar da Umaru Noma, Malam Usman Bachir kakakin Lumanar bangaren Noman ya ce matakin ba shi da wani tasiri a idon doka.

Koma dai mi ake ciki yanzu hankali ya karkata ga ma'aikatar ministan cikin gida wacce ita ce ke da hurumin bayyana wanda ya halitta a idon doka daga cikin wadannan tagwayen tarukan da bangarorin jam'iyyar ta Lumana suka gudanar. Bangaren da ma'aikatar ministan cikin gidan za ta amince da shi zai samu hurumin ajiye takardun ‘yan takaransa na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da kuma na kananan hukumomia gaban hukuma.

Sai dai akwai hadarin ma'aikatar ministan cikin gidan ta yi watsi da tarukan guda biyu kamar yadda ta taba yi a baya, wanda hakan zai haifar da matsala ga makomar jam'iyyar baki daya kasancewa kurewar lokaci ba zai ba ta damar sake tsayar da ‘yan takara ba a zabukan masu zuwa. Kazalika idan ma'aikatar cikin gidan ta amince da taron bangaren Hama Amadu, akwai hadarin takararsa ta fuskanci galubale a gaban kuliya.

Sauti da bidiyo akan labarin