An katse kafar internet a Jamhuriyar Nijar | BATUTUWA | DW | 24.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

An katse kafar internet a Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, kwana guda byan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato CENI ta bayara da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasa zagaye na biyu, hukamr ta ce kotun koli ce za ta bayar da sakamakon karshe.

Niger Protest gegen Ergebnis der Präsidentschaftswahl

Zanga-zanga bayan bayyana sakamakon zaben wucin gadi

Za dai za a iya cewa tuni bangaran dan takara Bazoum Mohamed duk da cewa ba su samu damar walwala ba sun nuna farincikinsu. Sai dai zanga-zanga ta barke a Yamai babban birnin kasar, tun daga yammacin Talatar da ta gabata ya zuwa cikin daren Laraba, lamarin da ake ganin ya sanya hukumomin kasar katse kafar internet.

Karin Bayani: Kira kan karbar sakamakon zabe a Nijar 

An dai wayi gari kamar kura ta lafa sai kuma matasa masu zanga-zangar suka sake fitowa cikin unguwanni, inda suke kone-kone da kuma rufe tituna. Tuni dai jami'yan tsaro suka fito ko'ina domin dakile masu zanga-zangar, ta hanyar harba musu borkonon tsohuwa da kuma kame wadansu. Sai dai wannan lamari na rashin Internet bai hana fitowar jama'a cikin unguwannin ba, inda suke iya yin kiran waya.

Nigeria Lagos junge Männer mit Smartphones

Rayuwar matasan Afirka, ta fara dogara kan kafar internet

Lamarin dai ya fi shafar rayuwar matasa da suka dade da sabawa da shafukan internet din, inda ta nan ne suke dukkannin wata hulda da kuma bincike na karatu ga daliban jami'o'i. Dama dai an yi hasashen samun rikicin bayan zabe, muddin dai wani daga cikin bangarorin biyu na masu mulki ko adawa ya bayyana cewa ba a yi masa daidai ba a lokacin zaben ko kuma bayar da sakamakon zaben. A cewar Mahamane Sani kusa a bangaran 'yan adawa na CAP 20/21 da suka goyawa Mahamane Ousmane baya, shekaru da dama bai ga irin wannan yanayi ba.

Karin Bayani: Wacce alkibla siyasar Nijar ta dosa?

A halin yanzu dai za a iya cewa lamura na kara kamari, inda matasan da ke kone-kone ko toshe hanyoyi suke nuna ba su da alamar sassauci kan fushin da suke nunawa. Ana dai ganin ya kyautu a samu nutsuwa kamar yadda masu sa ido kan zaben suka riga suka fada a cikin sanarwoyinsu, cewa ya kyautu a damka komai a hannun kotu wadda za ta yanke hukunci. Koda yake 'yan adawar sun ce ko a zagayen farko ma, kotun watsi ta yi da kararrakin da suka shigar a gabanta.

Sauti da bidiyo akan labarin