1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Matakan dakile tarzoma yayin zabe

February 19, 2021

Kwamitin kula da tsaro a harkokin zabe ya sanar da daukar matakai domin dakile matsalolin ta'addanci ko tarzoma ta cikin gida a lokacin zaben shugaban kasa zagaye na biyu

https://p.dw.com/p/3pcXg
Bildkombo I Präsidentschaftswahlen in Niger qualifiziert haben: Mohamed Bazoum und Mahamane Ousmane

A bahasin da kwamitin kula da tsaro a harkokin zaben kasar ta Nijar ya bayar a gaban masu sa ido a harkokin zabe na ciki da na waje, ya bayyana cewa sun tantance wasu manyan matsaloli guda uku da ka iya zama barazana ga zaben na ranar Lahadi. Babba daga cikin wadannan matsaloli ita ce ta yiwuwar fuskantar hare-haren 'yan ta’adda a wasu yankunan kasar kamar yadda ta kasance a zabbukan da suka gabata. Kanal Manjo Bako Boubakar shi ne shugaban kwamitin tsaro a harkokin zaben kasar ta Nijar.

Niger Niamey | Wahlen
Wata mai zabe a YamaiHoto: Issouf SANOGO/AFP

"Akwai mutanen da suka lashi takobin ganin bayan kasashenmu, kuma daya daga cikin hanyoyin da suke bi wajen ganin sun cimma wannan buri nasu, shi ne hana wadannan kasashe namu samun zababbun shugabanni, wannan kuwa ta hanyar hana gudanar da zabe. Suna iya kokarinsu domin su hana kai akwatunan zabe a garuruwa, har ma su kan yi wa masu garuruwa barazanar kisa idan suka yarda aka shirya zabe a garuruwan nasu"

A game da wannan barazana ta ‚yan ta’adda kwamitin zaro a harkokin zaben kasar ta Nijar ya sanar da cewa sun dauki matakai na dakile matsalar.

"Ya ce mun samar da jami’ai sama da dubu 35 da motoci kimanin 5,000 da babura 200 da jiragen sama guda biyar da kananan jiragen ruwa na soja domin tabbatar da tsaro a wannan zabe. Dukkannin cibiyoyin hukumar zabe a kananan hukumomi 266 an girke jami’an tsaro sannan an yi cikakken tanadi domin tsaron lafiyar shugabannin zaben a kananan hukumomi 266  an kuma baza jami’an tsaro a dukkanin cibiyoyin zabe dake birnin Yamai."

Niger Niamey | Wahlen
Aikin zabe a birnin Yamai Hoto: Issouf SANOGO/AFP

Sai dai Wata matsalar da ke ci wa mahukunta tuwo a kwarya a tafiyar da wannan zabe ita ce ta rikici a tsakanin 'yan siyasa wanda kwamitin tsaron ya ce yana iya haifar da rikici a lokacin zabe ko kuma bayan zabe, amma kuma sun dauki matakan kandagarki

Kwamitin tsaron kan harkokin zaben ya kuma nuna damuwa kan yadda magoya bayan 'yan takarar biyu ke amfani da shafukan sada zumunta wajen yada abubuwan da ke zafafa yanayin siyasar kasar da kuma ka iya haddasa tashin hankali. Akan haka kwamitin ya yi kira ga duk masu fada a ji a cikin kasa da su ba da tasu gudunmawa wajen canza wannan mummunan tunani domin ganin zaben ya gudana a cikin kwanciyar hankali da lumana.