Nijar: An fitar da Hama Amadou zuwa Faransa | Labarai | DW | 09.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: An fitar da Hama Amadou zuwa Faransa

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun sahalewa madugun adawar kasar tsohon Firaminista Hama Amadou fita daga gidan kaso zuwa kasar Faransa domin neman lafiya.

Abdou Rafa da ke magana da yawun tsohon firaministan na Jmahuriyar Nijar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa tun a ranar Laraba Hama Amadou ya isa Faransa kuma zai kwashe makonni biyu ne yana jinya kafin daga bisani hukumomi su sake dawo da shi gidan kaso.

A ranar daya ga watan Maris da ya gabata ne dai hukumomi Jamhuriyar Nijar suka tura tsohon firaministan gidan yarin Filingue bayan da aka zarge shi da hannu wurin haddasa rikicin bayan zaben shugaban kasar da ya gabata. Hukumomi na zargin Hama Amadoun da kasancewa kanwa-uwar-gami a zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaben da dan takarar adawa Mahamane Ousmane ya yi.