Nijar: Madugun adawa daga jam'iyyar Lumana | Siyasa | DW | 08.02.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Madugun adawa daga jam'iyyar Lumana

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya nada Tahirou Seidou shugaban jam'iyyar adawa ta Hama Amadou Lumana Afirka, a matsayin sabon madugun adawar kasar.

Nigeria I Shugaba Mohamed Bazoum

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum

Sai dai jam'iyyar ta Hama Amadou wato Lumana Afirka, ta ce ita har yanzu gwamnati ba ta tabbatar mata da wannan matsayin a hakumance ba. A bangare guda kuma matakin ya fara haifar da muhawara, dangane da wanda ya dace ya zama madugun adawa a tsakanin 'yan adawar kasar. A cikin wani kudiri wanda shugaban kasar Nijar din ya dauka tun ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata ne, ya tabbatar da nada Tahirou Seidou shugaban jam'iyyar ta Lumana Afirka a matsayin sabon madugun adawar kasar.

Karin Bayani: Shawo kan kalubalen dimukuradiyya a Nijar

Kamar yadda doka ta tanada kudin da za a biya shi a jimlace tsakanin albashi da kudin haya da na wuta da ruwa da sauran hidimomi na gidansa da fadarsa, zai samu kudi kusan miliyan daya da jaka 800 na CFA, kuma gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum ce za ta biya shi kudin. Kazalika dokar ta tanadi ba shi ofishi na musamman da kuma fasfo na diplomasiyya shi da matansa da daukar nauyin kula da lafiyarsa da ta iyalansa, ko kuwa ta kama za su je neman magani a ketare.

 Hama Amadou

Hama Amadou ne dai jagoran adawa a Jamhuriyar ta Nijar

Da take tsokaci kan matakin nada sabon Madugun adawar kasar ta Nijar, jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki, ta bakin kakakinta Malam Adamou Manzo ta bayyana alfaharinta da yadda gwamnati ta mutunta doka. To sai dai duk da cewa sakatariyar gwamnati ta tabbatar da sahihanci kudirin nadin madugun adawar, daga nata bangaren jam'iyyar Lumana Afirka ta bakin babban magatakardanta Malam Maman Sani  ta ce kawo yanzu ba za ta ce komi ba kan nadin domin kuwa ba a aiko mata da takardar nadin a hakumance ba.

Karin Bayani: Sasanta rikicin siyasa a Jamhuriyar Nijar

Abin da Malam Adamou Manzo na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mullki ya ce ba zai rasa nasaba da sabanin da wasu ke zargi ana fuskanta tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta Lumana Afirka kan wanda ya dace a bai wa matsayin madugun adawar daga cikin shugabanninta ba. Kokarin jin ta bakin sabon madugun adawar dai ya ci tura, inda wasu daga cikin mukarrabansa suka ce yana cikin zaman makoki na wani dan uwansa da ya rasu dan haka ba shi da damar yin wata magana ta siyasa a yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin