1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar: Sasanta rikicin siyasa

Mahaman Kanta LMJ
October 13, 2021

An fara wani zaman taron neman hanyoyin shinfida zaman lafiya na tsawon kwanaki biyu a Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/41dlk
Niger Protest gegen Ergebnis der Präsidentschaftswahl
Zanga-zanga ta barke a wasu sassan Nijar, bayan sanar da sakamakon zabe

Wannan taron dai na zuwa ne, sakamakon rigingimun siyasar da suka biyo bayan zabukan da aka gudanar a cikin watan Fabarairun wannan shekara ta 2021 da muke ciki. An dai gayyaci wakillan jam'iyyun siyasar ta Nijar bangarorin adawa da masu mulki da na kungiyoyin farar hulla da sarakunan gargajiya da malaman addinai, domin halartar wannan taro. Wata kungiya da ke bayar da agaji wadda gwamnatin Amirka ke tallafawa mai suna IMANI reshen Jamhuriyar ta Nijar ce dai, ta shirya wannan taron. Wasu daga cikin mahalarta taron dai, sun yi kira da a sako magoya bayan jam'iyyun adawa da aka kame.

Catoon Niger Wahl 2020
Wasu jam'iyyun adawa, ba su yi maraba da sakamakon zaben Nijar ba

Mafiya yawan wadanda aka kama ake tsare da su dai, matasa ne da suka fito kan tituna domin nuna adawarsu da sakamakon zaben da aka bayyana. A ta bakin wakinlin wata kungiyar matasa mai suna Adamu Hammadou yakamata a dauki matakan kare afkuwar ire-iren wadannan matsalolin, yana mai yin kira ga hukumar zabe da ta bai wa kowa hakkinsa sannan 'yan siyasa su wayar wa magoya bayansu da sauran mutanen kai dangane da ka'idojin zabe kamar yadda doka ta gindaya. Taron ya kuma gaiyato masanan zamantakewar yau da kullam da za su bayar da mukala, domin a dauki matakai kan sakamakon nazarce-nazarcen da aka yi saboda mangance wadannan matsaloli.