Kungiyoyi sun yi tir da tsare yara a Nijar | BATUTUWA | DW | 03.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kungiyoyi sun yi tir da tsare yara a Nijar

Bayan kazamar zanga-zangar bayan zaben kasa a Nijar, ana ci gaba da tsare daruruwan matasa da aka kama a lokacin boren, abin da masu fafutikar kare hakkin dan Adam ke yin tir da shi.

Sama da mutane 400 ne akasarin su matasa, mahukuntan kasar ta Nijar suka ce sun kame lokacin kazamar zanga-zangar da ta yi sanadiyyar asarar rayuka da ta dukiyoyi a birnin Yamai. Ko yanzu haka a kowace safiya, iyayen matasan na kai kawo wajen ganin ‘ya’yan nasu a inda ake tsare da su a makarantar horas da ‘yan sanda ta kasa da ke a birnin na Yamai.

Wasu daga cikin iyayen yaran da DW ta zanta da su a gaban cibiyar da ake tsare da yaran nasu, sun koka a game da halin da suka tsinci kansu su da ma yaran nasu. Sai dai kungiyar Mojen mai fafutikar kare hakkin dan Adam da dimukuradiyya a Nijar, ta bakin shugabanta, Malam Siraji Issa, ta zargi ‘yan siyasa da sanya matasan a cikin wannan hali kuma suka yi watsi da su.

To sai dai da yake mayar da martani a kan wannan zargi, Malam Habila Rabiou, daya daga cikin masu magan da yawun kawancen adawa na CAP 21, ya ce akasarin mutanen da aka kama, ba a wajen zanga-zangar ba ne kuma zargin da ake yi wa adawar ba shi da tushe; hasalima akwai ayar tambaya a kan halaccin karbar kudin beli da hukumomi ke yi kafin sakin yaran da ke tsare.

Wani jami’in dan sanda a wurin da ake tsare da mutanen da bai so a ambaci suansa ba, ya ce tun a jiya Talata aka sallami illahirin yaran da ba su wuce shekaru 13 ba daga cikin su, amma kuma za a gurfanar da sauran wadanda shekarunsu ya haura 14 a gaban kuliya domin zartar masu hukuncin da ya dace da laifin da suka aikata. 

Sauti da bidiyo akan labarin