Hari a kudancin jihar Bornon Najeriya | Labarai | DW | 30.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a kudancin jihar Bornon Najeriya

Ana fargabar mutane da dama sun rasu sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a garin Shani da ke kudancin jihar Bornon Najeriya.

Wakilinmu na Gombe Al-Amin Sulaiman Muhammad da ke bin diddigin labarin ya ce wadan suka tsira daga wannan hari sun bayyana cewa a daren jiya ne Asabar ce ‘yan bindigar suka afkawa garin dauke da muggan makamai da kuma bama-bamai inda suka bude wuta kan mutane ba kakkautawa.

Baya ga wanda maharan suka hallaka, a hannu guda sun kuma kona gidaje da ababan hawa da dama lamarin da ya tilasta mutane shiga cikin dazuka da garuruwa makota. Ya zuwa yanzu dai hukumomi ko jami'an tsaro ba su kai ga cewa komai kan harin ba.