Gwamnatin Jamus ta koma da ′yan Afghanistan 125 gida | Labarai | DW | 24.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Jamus ta koma da 'yan Afghanistan 125 gida

A makonnin bayan nan dai yawan 'yan gudun hijira daga Afghanistan da ke shigowa Jamus ya karu.

A wani abin da ke zama wata matsalar 'yan gudun hijira da take fuskanta, a karon farko Jamus ta koma da 'yan Afghanistan 125 gida. Tuni dai jirgin saman da ya kwashi 'yan gudun hijirarya isa birnin Kabul, inji ma'aikatar cikin gidan Jamus da ke birnin Berlin, wadda ta kara da cewa 'yan Afghanistan din sun koma gida ne don radin kai bayan an hana su takardun izinin zama a Jamus. Wata yarjejeniya da gwamnatin tarayyar Jamus ta kulla da mahukuntan Afghanistan ta tanadi mayar da masu neman mafakar siyasa da aka yi watsi da bukatunsu, gida. Jamus dai na mai ra'ayin cewa a Afghanistan akwai wurare masu tsaro da kwanciyar hankali da 'yan kasar wadanda suka tsere daga ta'asar Taliban, za su iya zama ciki. A makonnin bayan nan yawan 'yan gudun hijira daga Afghanistan ya karu.