Gwamnatin Bama ta yi Allah wadai da mamaye Iraqi da Amirka ta yi. | Labarai | DW | 16.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Bama ta yi Allah wadai da mamaye Iraqi da Amirka ta yi.

Kafofin yaɗa labarai na gwamnatin ƙasar Bama sun yi kakkausar suka ga mamayar da Amirka ke yi wa Iraqi. A cikin wani sharhin da ta buga yau, jaridar nan „New Light of Myanmar“ ta gwamnati, ta ce harin da Amirka ta kai wa Iraqi na tabbatad da cewa matakan sanya wa wata ƙasa takunkumi da kuma afka mata, ba hanyoyi ne na dimukraɗiyya ba. Bugu da ƙari kuma, ta ce ruɗamin da ake ciki a Iraqin a halin yanzu dai na nuna cewa, ba haka kawai ne za a iya cusa wa wata ƙasa ra’ayoyin dimukraɗiyya da kuma tilasa mata ta rungume su ba. Jaridar dai ta bayyana shakkun cewa, gwamnatin ’yan amshin shatan Amirka ta ƙasar Iraqin, ba za ta taɓa iya tabbatad da tafarkin dimukraɗiyya a ƙasar ba.