1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel a idanun George W. Bush

Ines Pohl RG/LMJ
July 14, 2021

Ba kasafai tsohon shugaban Amirka, George W. Bush ke hira da manema labarai ba, amma saboda kyawun alakarsa da Angela Merkel ta Jamus, Bush ya gayyaci DW har gidansa.

https://p.dw.com/p/3wTU6
Merkel zu Besuch auf George W. Bushs Ranch in Texas
Akwai kyakkyawar alaka tsakanin Angela Merkel da George W. BushHoto: Matthew Cavanaugh/dpa/picture-alliance

Tsohon shugaban Amirkan George W Bush ya gayyaci tashar DW din ne, domin tattauna batutuwan da suka auku a lokacin da shugabanin biyu suka yi aiki tare da ma siyasar duniya. Wakiliyar DW a birnin Washington Ines Paul, ta fara tambayar Bush din wane sabani suka taba samu a lokacin da ya ke shugabancin Amirka da ba zai taba mantawa ba?

"Batun cancanta a bai wa Jojiiya damar zama mamba a kungiyar tsaro ta Nato. A nata ganin bai dace ba, ni kuma a tawa fahimtar ya dace. Daga karshe ba mu saka son zuciya a ciki ba, ai siyasa ce. Daga baya babu wani abun tashin hankali, ba na jin an sami wani sabani da har za a ce ta kai ga daya na neman afuwar daya da sunan wani yunkuri na gyara dangantakarmu."

Deutschland Merkel Selfie mit Anas Modamani
Hoton da Merkel ta dauka da dan gudun hijira, ya dauki hankali a 2015Hoto: Getty Images/S. Gallup

A tsawon jagorancin Merkel wani batu da ya ja hankulan kasashen duniya shi ne matakin Merkel na bude kofofin Jamus, inda ta bai wa 'yan gudun hijira kimanin miliyan daya mafaka, ya ka ji kan matakin nata da ake wa kallon wani babban babi a tarihin shugabancinta?

"Da farko, abin da ya zo min rai shi ne ga mace mai imani. Na tabbatar cewa, tausayi ne ya saka ta daukar matakin. Na jinjina mata, mace ce da ba ta tsoro ta gudanar da sha'anin mukinta. Tana da jarumta duk da cewa ta fuskanci kalubale, a tsawon shugabancintan na fiye da shekaru 16. Saboda haka koda akwai wadanda ba su yarda da wasu tsare-tsarenta ba, babu shakka ana mata kyakyawan zato an kuma yarda da ita. Fiye da komai, mutuniyar kirki ce."

Akan batun janye rundunar Amirka da ta kungiyar tsaro ta Nato da suka kwashe shekaru akalla 20 a kasar Afghanistan kuwa, tsohon shugaban kasar Amirkan ya ce matakin wani babban kuskure ne da ka iya jefa rayuwar wadanda ba su ji ba su gani ba cikin hadari.

George W. Bush im DW Interview mit Ines Pohl
Tsohon shugaban Amirka George W. Bush yayin tattaunawa da Ines Pohl ta DWHoto: DW

"Na yarda kuskure ne, don na san abubuwan da za su biyo baya ba za su yi kyau ba. Shi yasa na ke cike da takaici, ina cike da fargabar makomar wadanda suka jima suna wa sojojin Nato aikin tafinta da wadanda suka taimaki rundunar sojojin Naton. Yanzu duk an bar su, kuma ga dukkan alamu azzaluman nan za su bisu daya bayan daya suna yi musu yankan rago. Lamarin na sare min zuciya."

Daga karshe tsohon shugaban kasar ta Amirka George Bush ya fadi ra'ayinsa kan shugabancin Angela Merkel da ke shirin kawo karshe, a cikin annushuwa ya bayyana ta a matsayin mace jaruma ce da ta gudanar da shugabancin na gari.

"Ita..ina zaton martaba da tsarin da ta gina shugabancinta a kai, na san da wuya yanzu a gane hakan kila sai daga baya kafin tarihi ya tabbatar da nasararta. Idan aka ce shugabanci da misali yanzu ake rashin hali na gari, amma Angela Merkel ta zama abar kwatance kan shugabanci na gari. Shugaba ce da na ke alfahari da ita, saboda tana birgeni.''