Sharhi: Merkel za ta ci gaba da mulki | Siyasa | DW | 09.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Merkel za ta ci gaba da mulki

Jam'iyya mafi girma a Jamus ta zabi ta hannun damar shugabar gwamnati Angela Merkel, Annegret Kramp-Karrenbauer a matsayin wadda za ta karbi shugabancin jam'iyar. Babbar editar DW Ines Pohl ta rubuta sharhi a kai.

Kasashen ketare basu cika damuwa da zaben wani muhimmin jami'i a wata jam'iyyar Jamus ba. Amma a wannan karon ba haka lamarin yake ba. A cikin 'yan kwanakinnan manyan jaridu na duniya kamar su New york Times sun rewaito batutuwa da dama kan taron jam'iyyar ta Merkel ta Christian Demokrat watau CDU, fiye da batun jana'izar tsohon shugaban Amurka George H.W. Bush.

Kallo ya koma kan Jamus. Gidajen talabijin sun kasance cikin yanayi na bada labari da dumu duminsa lokacin da aka zabi sabuwar shugabar jam'iyyar CDU. Hakan kuwa na faruwa ne saboda Angela Merkel. Ga mutane da yawa dai, shugabar gwamnatin na Jamus ta kasance zakara fagen siyasar duniya. Duba da cece ku ce da ke cigaba da mamayar manyan 'yan siyasa kamar shugaban Rasha Vladimir Putin da na Amurka Donald Trump da Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya.

Ana yi wa Merkel kallon 'yar siyasa mai alkibla, mai samar da daidaito a daidai lokacin da rarrabuwar kawuna ya yi kamari, sakamakon bunkasar akidar kyamar baki. Sai dai a cikin kasarta, tauraron Merkel na dusashewa. A zaben jihohi, jam'iyyarta ta sha kaye a matakai daban daban. Suka da ta cigaba da samu daga cikin nata jam'iyyar kazalika ya sa Merkel ta dauki matakin yar da kwallon mangoro ta huta da kuda.

Mai sharhi: Ines Pohl

Mai sharhi: Ines Pohl

Lokacin da sanarwar ta fito a karshen watan Oktoba, lokacin ne fafutukar neman mai maye kujerar ta taso. Duk da cewar wa'adinta ba zai kare ba sai nan da wasu shekaru biyu da rabi, a bayyana take cewar ba zata iya cigaba da jagoranci ba, idan har jam'iyyar ta zabi daya daga cikin masu adawa da ita zuwa wani babban mukami.

Mutumin da Merkel ta kora daga kujerar shekaru takwas da suka gabata Friedrich Merz, ya yi asasar damar da ya jima yana jira na ramawa kura aniyarta da kuri 35 daga cikin adadin 1001. Duk da kuwa goyon bayon bayan da ya samu daga mazajen da Merkel ta yi gefe da su a tsawon lokacin da tayi tana shugabanci.

Bayan tsawon ranar da ta soma da jawabin Merkel cikin alhini, sakamakon ya fito. Annergret Kramp-Karrenbauer ce ta samu nasara. Da wannan nasararce taron ya kada kuri'ar amincewa shugabar gwamnatin ta karasa wa'adinta na mulki, matukar karamar jam'iyyar SPD da suke hadaka da ita bata fice daga gwamnatin ba.

Hakan dai na nufin manufofin ketare na Jamus  zasu cigaba da zama a bun dogaro, kazalika tattalin arzikinta, kasancewar da wuya manufofin gwammnati su sauya. Acikin gida kuwa za'a ga irin rawar da Kramp-Karrenbauer za ta taka wajen cimma nasarar sake samar da hadin kan bangarori daban daban na jam'iyyar, bisa la'akari da cewar ba wai jam'iyyarsu ta CDU kadai ba amma har da Jamus din ita kanta, na bukatarsa cikin gaggawa.

A yanzu haka dai CDU na da mata biyu da ke shugabancinta amma ba daya ba

Sauti da bidiyo akan labarin