1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janye sojojin Amirka daga Afghanistan

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 2, 2021

Amirka da kungiyar Tsaro ta NATO, sun janye baki dayan sojojinsu daga babban sansanin sojojin kasa da kasa da ke ksar Afghanistan.

https://p.dw.com/p/3vxHe
Nato Truppen verlassen Afghanistan
Amirka ta jima ta na batun janye sojojinta daga AfghanistanHoto: Vyacheslav Oseledkov/AFP/Getty Images

Wani babban jigo a rundunar sojojin Amirkan ne ya bayyana hakan, inda ya ce baki dayan sojojin hadakar na kasa da kasa sun bar sansanin nasu da ke Bagram. Rahotanni sun nunar da cewa tuni aka mika sansanin ga sojojin Afghanistan din. Shugaban Amirka Joe Biden ya bayyana cewa, sojojin kasarsa za su bar Afghanistan a ranar 11 ga watan Satumbar wannan sshekara, a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 20 da kai mummunan harin ta'addanci a Amirkan da ya haddasa asarar dimbin rayuka da dukiyoyi.