Ganawa tsakanin shugaban Amirka da na Rasha | Labarai | DW | 19.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawa tsakanin shugaban Amirka da na Rasha

Fadar mulkin Amirka ta tabbatar da ganawa ta biyu tsakanin shugaban kasar da na Rasha lokacin taron kungiyar G20.

Fadar mulkin kasar Amirka ta White House ta tabbatar da cewa Shugaba Donald Trump ya yi ganawa ta biyu da Shugaba Vladimir Putin na Rasha a farkon wannan wata na Yuli. An yi tattaunawar a gefen taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da ya gudana a birnin Hamburg na Jamus.

Wannan ke zama karon farko da aka samu bayani kan ganawar, bayan ganawa ta farko tsakanin shugannin biyu ta dauki hankalin kafofin yada labarai na duniya. Ita dai wannan ganawa ta biyu tsakanin Shugaba Trump na Amirka da Shugaba Putin na Rasha an shafe kimanin sa'a guda.

Tuni shugaban na Amirka ya caccaki kafofin yada labarai da suke neman bayar da labarin wani kormato da aka samu.