Gagarumin sumame a kan Boko Haram | Labarai | DW | 02.04.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gagarumin sumame a kan Boko Haram

Dakarun Kasashen Nijar da Najeriya da Chadi sun girka kawance hadin gwiwa da nufin kawar da Boko Haram da ke dada kai hare-hare a kasashen.

Dakarun Kasashen Najeriya da Nijar da kuma Chadi sun kaddamar da wani gagarumin sumame na hadin gwiwa da nufin kawar da kungiyoyin Boko Baram da ISWAP wadanda suka dada kai hare-hare a kan sojojin kasashen a 'yan kwanaki nan. A cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Njeriya ta bayyana ta ce bukatar hadin gwiwar na sojojin kasashen na yankin tafkin Chadi ya zama wajibi domin cimma nasarar yaki da Boko Haram. A cikin watan Maris da ya gabata mayakan na Boko Haram sun kashe sojoji sama da 100  a Chadi da kuma Najeriya.