1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fargaba kan makomar kudin CFA bayan zaben Senegal

March 28, 2024

Zaben dan takarar adawa a matsayin shugaban kasar Senegal ya haifar da fargaba da rashin tabbas kan makomar kudin CFA da ke zama kudin bai daya na kasashen Yammacin Afrika.

https://p.dw.com/p/4eCpi
Banknoten CFA Francs
Hoto: SEYLLOU/AFP

A lokacin yakin neman zaben Senegal kawancen da ya kawo Bassirou Diomaye Faye mai shekaru 44 a duniya kan karagar mulki ya yi kakkausar suka ga kudin CFA da kasashen UEMOA suka gada daga kasar Faransa da ta yi musu mulkin mallaka, sannan ya kuma nuna goyon bayan ra'ayin samar da takardun kudi na yankin yammacin Afrika watau ECO, wanda aka yi alkawarin samarwa a shekarar 2027.

Kawacen da ke shirin kafa sabuwar gwamnati a Senegal da ke zama jigon tafiya a kasashen da ke amfani da kundin CFA ya kuma yi barazanar samar da sabbin takardun kudi ga kasar muddin aka samu jinkiri wajen samar da ECO

Kyamar siyasar Faransa da ke karuwa a tsakanin matasan wasu kasashen yammacin Afrika da kuma raguwar tasirinta a nahiyar na daga cikin ababan da suka janyo wa takardun kudin CFA bakin jini.

Karin bayani: Nijar: Takaddama kan amfani da kudin CFA

Dama dai a watannin da suka gabata kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar da ke karkashin mulkin sojoji sun nuna kosawa da takardun kudin na CFA da ake bugawa a Faransa tare da juya baya ga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika watau ECOWAS ko kuma CEDEAO.