Najeriya ta soki batun canza CFA zuwa ECO | Labarai | DW | 16.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ta soki batun canza CFA zuwa ECO

Najeriya da wasu kasashe na yammacin Afirka sun soki lamirin matakin da wasu kasashen ECOWAS suka dauka na yin gaban kansu wajen sauya kudin CFA zuwa ECO a shekarar badi.

A sanarwar da suka fitar a karshen wani taro da suka shirya a wannan Alhamis a birnin Abujan Najeriya, ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kasashen Najeriya da Ghana, Laberiya, Saliyo Gambiya, da kuma Guinea Konakry da ke zama kasa daya daga cikin masu amfani da kudin CFA da ta halarci taron, sun yi tir da Allah wadai da matakin da wasu kasashe mambobin kungiyar ECOWAS na yin gaban kansu wajen sauya kudin CFA zuwa ECO nan zuwa shekara ta 2020.

 Kasashen shida da suka halarci taron na birnin Abuja sun ce matakin da sauran 'yan uwan nasu suka dauka ya saba wa yarjejeniyar da kungiyar ECOWAS ta cimma ta samar da kudin bai daya a tsakaninsu.

 Sun kuma jaddada bukatar ganin illahirin kasashen na ECOWAS su mutunta jadawalin da Shugabannin kasashen na CEDEAO suka tsaida a kan batun samar da kudin na bai daya. An tsaida cewa nan ba da jimawa ba shugabannin kasashe shida masu magana da Inglishi za su gudanar da taro domin fitar da matsaya kan batun.